Shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya Amaju Pinnick, ya bayyanar da gudunmawar shi, wajen ganin an kauda tsohon shugaban kungiyar kwallon kafar Afrika CAF Issa Hayatou, dan asalin kasar Cameroon wanda ya kwashe tsawon shekaru 29, yana jagoranci kungiyar.
Ya gabatar da wannan jawabin ne a lokacin da yake gabatar da kasida, a taro na 2 da jami’ar tunawa da Michael da Cecilia Ibru, suka gabatar a jihar Delta, jiya Talata. Ya kara da cewar akwai yunkurin sake sabunta matsayin Hayatou, a matsayin shugaba na karin wani wa’adi.
Na bada tawa gudunwa daga farko har zuwa karshen zaben, duk da cewar mambobin kungiyar, sun tsaya tsayin daka kan cewar, idan ba Hayatou ba babu wani. A yayin zaben da aka gabatar, amma abun sha’awa shine, mafi akasarin mutane suna son ya tafi.
Don ta haka ne kawai za’a ba wasu damar baje irin tasu basirar. A makon da ya gabata ne, shugaban kungiyar kwallon kafar jihar Delta, ya bayyanar da cewar, ya dauki babbar kasada, a lokacin da ya nuna rashin aminta da tsohon shugaban kungiyar ta Afrika a yayin gudanar da zabe.
Sai ya kara da cewar, gaskiya daukar Mr. Gernot Rohr, da akayi a matsayin mai horas da ‘yan wasan Super Eagle, shima kasadane, duk dai da cewar mafi akasarin kocis da ake dauka daga Najeriya, basu iya yin wani rawar gani ba.
Amma zuwa yanzu, Mr. Rohr, ya fara nuna cewar ya shirya daukaka kungiyar a duniya, ba za’a kara tabbatar da hakan ba, har sai idan Allah yasa ‘yan kungiyar sun samu tikitin shiga, jerin sahun wadanda zasu buga wasan gasar cikin kofin duniya.