Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Zai Kwashe Shekaru Biyu A Gidan Yari Saboda Satar Shinkafa


Wata Kotun a Osogbo, babban birnin jihar Osun, ta yakewa wani matashi Fatai Ganiyu, mai shekaru ashirin da tara da haihuwa zaman shekaru biyu, a gidan yari bayan da ta sameshi da laifin satar tiya goma na shinkafa/, da kwalba hudu na barasa.

Mai gabatar da karar Wilson, ya fadawa kotu cewa Ganiyu, ya fasa shagon wata mata mai suna Okeola Comfort, dake unguwar Ayepe, a Gbongan, da misalign karfe biyu na dare inda yayi awon gaba da kayayyaki.

A cewarsa wannan ya sabawa sashe na 283 da 414, karamin sashe na 34,na kundin laifuffukan jihar Osun, na shekara2002, wanda aka bayana hukumcin sa a sashe na 390 sakin layi na 9, a kundin laifuffukan.

Ganiyu, wanda lauya Seye Oluyombo, ya wakilta ya amsa laifinsa,

Shi kuwa mai shara’a, Adejumoke Olowolagba, bayan da ya amsa laifinsa tace yaje yayi shekaru biyu a gidan yari.

XS
SM
MD
LG