Mutane ma su bukata ta musamman a jihar Kano sun koka da irin yadda su ka ce hukumomi na yin kunnen uwar shegu dangane da walwalarsu a fannoni da dama.
Majalisar dinkin duniya dai ta ce wajibi ne ga gwamnatoci su tabbatar da cewa iyalan masu bukata ta musamman su sami ilimi da za su rika gogayya da sauran 'ya’yan ma su lafiya.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa a kasashe ma su tasowa abin ba haka yake ba, inda a lokuta da dama gwamnatoci ke watsi da rayuwar al’ummomin da ke da tawaya a jikinsu
Masu bukata ta musammam dai na cewa suna fuskantar koma baya a dukkanin al’amarurrukan da suka shafi cigaba da zamantakewa hakan ne ma ya sa da aka tashi bada mukamin babban mai baiwa gwamna shawara, ba’a ba mai nakasa ba.
Ga rahoton Baraka Bashir daga Kano.