Hukumar shige da fice ta Najeriya, ta cafke wani mutun da yake kokarin tsallakewa ta wasu ‘yan mata har su shida zuwa kasar Burkina Faso.
Shi dai wannan mutumin da aka cafke ya taho da wadannan ‘yan mata ne tun daga jihar Edo, ya biyo garin Saki, a jihar Oyo, mai iyaka da Cotonou, ta kasar Benin.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin shugaban hukumar shige da fice na rundunar dake kan iyakar Ekaete Isang, yayi korafi akan rashin hadin kai daga shuwagabanin al’uma, a garuruwan dake kan iyakoki a jihar inda al’umomin garuruwan ke taimakawa mutane wurin shiga da ficewa kasar ta hanyar da bata dace ba.
Ya kara da cewa hukumar ta sadu da masu ruwa da tsaki a irin wannan garuruwan amma, sakamakon ba wani abun azo a gani bane.
Su dai wadannan ‘yan mata da ake da niyyar kai su kasar Burkina Faso, domin aikin karuwanci tuni aka mika su ga iyayensu shikuma aka mika shi ga hukumar dake kula da fataucin bil-Adam.