Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Biyu Zasu Kwashe Shekaru Shida A Gidan Yari


Wata kotun dake zama a Benin dake jihar Edo, ta yankewa wasumatasa biyu daurin shekaru shida shida a gidan yari.

Matasan Happy Okotie, dan shekaru goma sha tara (19) da Kingsley Ebose dan shekaru ashirin da biyar (25), an samesu da laifin yin sata ne.

Alkalin kotun mai shara’a Racheal Ogbevon, ta yankewa matasan hukumcin zama a gidan yari na tsawon shekaru shida shida babu zabin tara.

Sun dai wadannan matasa an samesu da laifin fasa shago da sata,

Kayayyakin da suka sata sun hada da wayoyin hannu da kwamfuta watau (Laptop) da kudi Naira dubu goma sha bakwai.

Dan Sanda mai gabaar da kara Patrick Agbonifo, ya ce sun aikata laifin ne ranar 25, ga watan Agustan da ya gabata, ya kuma ce jimillar abinda suka sata sun kama Naira dubu dari biyu da talatin da biyar (235,000).

XS
SM
MD
LG