Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Cututtuka Da AKe Dauka A Sanadiyyar Canjin Yanayi!


Allurar Riga kafi
Allurar Riga kafi

A kowane yanayi da ake da shi, rani, kaka, bazara, hunturu, da ake samu a cikin kowace shekara, yanayin kanzo da wasu abubuwa na daban, wanda sukan shafi rayuwar dan’adam ta wurare daban-daban.

A lokacin bazara da ake tunkara, yanayi kan sa mutane daukar wasu cuttutuka, da kan iya zama hadari ga rayuwar dan’adam. Wani bincike da tarin masana suka gudanar, yayi nuni da wasu abubuwa da kan haifar da wasu cututuka, da batare da mutune sunyi la’akari da suba.

A lokacin da bishiyoyi suka fara kakkabar ganyayyaki, lokaci ne da wasu cututtuka ke fara yawo a cikin jama’a, kamar mura, tari, da wasu abubuwa makamantan su. Don haka yana da matukar kyau idan mutane zasu dinga amfani da abun rufe fuska, don kada kura ta shiga hanci ko bakin su.

Wanke gashi musamman cikin dare akai-akai, ga mata yana taimakawa wajen gujema kamuwa da kananan cututtuka. Wanka ko zama cikin ruwa masu tsafta na wani lokaci shima yana taimakawa wajen gujema cututtuka da dama.

Tsaftace hanci, a kowane hali na da matukar muhimanci, don ta nan ne cuta kanbi ta wuce, amma idan hanci na tsaftace, koda cuta tabi, bazata samu wajen zama ba. Don haka yana da matukar kyau, idan mutane zasu kokarta wajen daukar allurar riga kafi a cikin 'yan tsakanin nan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG