Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gabatar Da Wani Bukin Aure, Da Ba'a Taba Yin Irinshi Ba A Duniya!


Gadar Gilashi
Gadar Gilashi

Ana wata ga wata! Kowane dan’adam da irin bukin zuciyar shi, Mr. Jiang Huizhu da amaryar shi Zhou Wenlong, sun kafa tarihi, a ranar daurin auren su. Bayan an kammala shagulgulan buki, sun zabi suyi wani abu da babu ango da amarya da zasu tabayi a fadin duniya.

Sun sadaukar da rayuwar su wajen neman suna, inda suka tafi karkashin gadar gilashi ta farko a fadin duniya, suka saka zare da ya hada musu wurin zama kamar gado. Inda suka kwanta suna ta daukar hotuna, mutane na ta mamakin abun da su keyi. Angon ya bayyanar da cewar “Muna so mu nuna farincikin mune, ta wata hanya da babu wanda ya taba yi.”

Tsawon gadar da zaren da suka saka, ya kai kimanin mitoci dari da tamanin 180M, kwatankwacin bene hawa goma. Ita dai wannan gadar da aka yita, a cikin shekarar da ta gabata a cikin lambun hutu na “Shiniuzhai National Geological Park” a cikin kasar China, wurine na shakatawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG