Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Shekaru 20, Da Yafi Kowa Kudi A Kasashen Afrika!


Robert Mfune
Robert Mfune

A lokacin da nake makarantar sakandire, iyaye na basu da kudi ba kowace rana muke samun irin abincin da muke so ba. Mukan karbi kyautar abinci daga gwamnatin kasar Ingina, wanda ake ba talakawan kasar.

A lokacin da nakai dan shekaru sha bakwai 17, na fara aiki a gidan abincin tafi da gidan ka, na McDonald, inda nake samun kwabo da sisi, da haka har na samu na tara kudin makaranta. A dai-dai lokacin da na kai shekaru 18, sai na fara aiki a wani ofisi, inda nake bama ma’aikatan shayi.

Duk na kanyi wannan aikin a lokacin da bana makaranta, a wajen aikin na hadu da mutane da dama, da suke bani shawara kan cewar, nayi amfani da yarunta na don nazama wani abu a rayuwa, wannan maganar itace ta dinga tsaya mun a rai, har na fara tunanin ya zanyi nazama mai dogaro da kaina.

Daga aiki a gidan abinci zuwa bada shayi, zuwa karatu, da kokarin tsara ma kaina rayuwa, yanzu na mallaki billiyoyin kudi, kuma shekaru na ashirin 20. Ina da gidaje a kasar Ingila da kasata ta asali Afrika ta kudu, mahaifiya ta bata da matsalar komai, domin kuwa na saya mata gida da motar kimanin naira milliyan hamsin da biyu N52,000,000.

Babban abun da na fahimta da rayuwa shine, babu abun da mutun ba zai iya zama ba, idan ya sama kanshi zuciyar yi, musamman a lokacin da mutun yake matashi. Wannan shine labarin Robert Mfune, haifaffen kasar Ingila, dan asalin kasar Afrika ta kudu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG