Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Dan Bautar Kasa NYSC, Da Abokan Sa 3 Sun Kwanto Kura


Ranar litini Jami’an ‘yan sanda masu sintiri da ake kira Operation Lafiya Dole, a birnin Maiduguri, jihar Borno sun kama wasu matasa guda hudu da ake zargi da laifin bata dukiyar kasa.

Jami’an ‘yan sintirin sun kama Aliyu Jubril mai shekaru 24, da haihuwa wanda yake cikin bautar kasa wato NYSC, da Isma’ila Baba, mai shekaru 22, da haihuwa wanda yake makaranta a makarantar kimiyya da fasaha ta Ramat Polytechnic, da Muhammed Suleiman mai shekaru 25, shi kuma direba ne, da kuma Mohammed Bukar mai shekaru 15, wanda yake taimakawa direban, a ma’aikatar Silo dake kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, yayin da suke yunkurin datse manya manyan wayoyin lantarki da suka bata na kamfanin wutar lantarki na kasa.

Mujallara Daily post ta wallafa cewa mai magana da yawun jami’an soji kanar Sani Usman, a jawabinsa ya bayyyana cewa matasan da ake zargin sun yi amfani da babbar mota mai lodi inda suka loda tarin wayoyin a babbar mota.

Ya kara da cewa daya daga cikin matasan yaje wurin da karamar mota Honda kirar 2001.

Jami’an sun yiwa wadanda ake zargin tambayoyi, kuma za’a mika su ga jami’an da suka dace domin shara’anta su.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG