Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: An Gudanar Da Wasannin Tunawa Da Zagayowar Ranar Olympic Ta Duniya


A jamhuriyar Nijar, matasa da kungiyoyin wasanni sun gudanar da wani jerin gwano a wani fili da ake kira Is'haka Dabore Boxing club dake birnin Niamey inda suka soma bukin tunawa da ranar Olympics ta duniya wacce ke matsayin ranar kara hada kan masu hannu a sha’anin wasannin motsa jiki.

A albarkacin wannan rana, shugaban kwamitin Olympics reshen jamhuriyar Nijar Alhaji Ideh Isiyaka, ya gabatar da sakon shugaban kwamitin na Olympics na duniya Mr Thomas, inda ya ce lokacin wasannin Olympics lokaci ne na fadakar da jama’a amfanin motsa jiki, musamman matasa ta yarda zasu mayar da hankali akan motsa jiki.

Dan haka ya zama wajibi abi duk hanayar da za’a bi domin samun nasarar ganar da matasa cewar su aje na’urorinsu na kwamfuta, da wayoyin hannu, su fara motsa jiki domin abin ya zame masu jiki.

Bikin na wannan shekarar ya bada damar bude taron wani kwamitin da ma’aikatar ministan wasannin motsa jiki ta kafa da hadin gwiwar masu hannu a sha’anin wasanni a watan maris din da ya gabata, domin nazari akan hanyoyin da zasu taimaka a kaddamar da ayyukan wannan kwamiti mai alhakin sasanta rikici da wata baraka tsakanin kungiyoyi.

Ministan wassanni da motsa jikin kasar ya ce wannan wani gimshiki ne ga shirin rigakafin duk wata barkewar rikici ko daukar matakan warware takaddama, lamarin da zai bada damar sasanci Tsakani duk wasu masu motsa jiki ba tare da an kai batun gaban kotu ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG