Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Zata Kai Labari Kuwa A Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa Na Duniya



Akokari da Ghana take yi don shiga gasar cin kofin duniya a karo na hudu a jere, ta tsinci kanta a cikin rukunin ‘E’ a wasannin shiga gasar cin kofin duniyar na 2018 tare da Egypt, Congo da Uganda.

Ghana ta dauki kofin Afrika sau hudu, ta fara shiga gasar cin kofin duniya a karon farko a shekaran 2006. Kasashen da zasu kara da Ghana a rukunin ‘E’ sanannu ne a wurin Ghana wadanda suka yi wasanni a cikin wannan lokaci na neman gurabun a manyan gasa.

Tarhihin wasanni tsakanin Ghana da Congo, kasashen biyu sun hadu sau goma, Ghana ta doke Congo sau takwas, suki kunnen doki sau daya sa’annan Congo ta ba Ghana kashi sau daya.

Ghana ta doke Uganda sau shida a cikin haduwa sau goma sha biyu da suka yi ita kuma Uganda ta ci sau uku kuma suka yi baram baram sau uku

A cikin haduwa sau ishirin da Ghana tayi da Egypt Ghana ta sha kashi sau goma, taci biyar kuma suka yi baram baram sau biyar.

Duk da cewar Egypt tana da tarihi mai inganci akan Ghana, baki dayan wasan kwallo a nahiyar Afrika, mafi tarin ‘yan Ghana na kyautata zaton cewa Ghana zata iya samun gurbin shiga gasar cin kofin duniyar a Rasha, ganin cewa Egypt din ce kasa ta karshe da Ghana ta doke ta samu gurbin gasar duniya ta 2014 da aka yi a kasar Brazil, cikin rukunin ‘E’ a wasannin shiga gasar cin kofin duniyar ta 2018 tare da Egypt, Congo da Uganda.

XS
SM
MD
LG