Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yasa 'Yan-mata Su Kafi Yarda Da Samari Akan 'Yan'uwan Su Mata?


'Yan mata
'Yan mata

Kawance tsakanin mace da na miji, wani abune da yake da tsohon tarihi da kuma ma’ana, musamman idan an kulla kawance ta yadda ya kamata. Haka da mutunta juna. Dr. Joan Borysenko, likiti ne mai binciken hallayan dan’adam a jami'ar Adelaide, a kasar Australia.

Ya bayyanar da sakamakon wani bincike da ya gudanar da ya dauke shi tsawon shekaru goma. Ya iya gano cewar ‘yan mata sun fi samun natsuwa da kwanciyar hankali a lokacin da suke kawance da namiji, bisa kawancen su da ‘yanmata. Ya kara da cewar, mafi akasarin mata suna son kawance da maza don wasu abubuwa ne.

Samari suna da rikon amana idan mace ta basu amana, wanda baza su fada ma wani ba, amma idan mace ta ba mace yar’uwarta amana, da yawa sukan ci amanar. Idan mace ta yarda da namiji, babu abun da bata fada mishi koda kuwa ba saurayin ta bane, aboki ne kawai. Mafi akasarin maza sukan kyautatama ‘yan mata koda kuwa zasu bata ma ‘yan uwansu da abokan su basu damu ba.

Ya kara da cewar, kwakwalwar mata nada wani rukuni da maganar namiji ce kawai take shiga, don wani tasiri a rayuwar ta, shi yasa suke haukacewa idan suka samu rashin jituwa da samarin su. Su kuwa maza suna iya jurema kowane irin abu ne zai fito daga ‘yan matan su. Amma wajen kyautatawa maza sunfi daukan lokacin su, sosai don kyauatata ma ‘yan mata batare da tunanin wani abu da zai biyo baya ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG