Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawakiyar Amurka, Ta Zabi Zama 'Yar Najeriya Fiye Da Kasar Ta!


Mawakiya Keri Hilson
Mawakiya Keri Hilson

Shahararriyar mawakiyar kasar Amurka, Keri Hilson, ta bayyanar da zunzurutun kaunar da take ma kasar Najeriya. Ita dai haihaffiyar jahar Georgia ce a kasar Amurka. Tana auren wani dan Najeriya, Samuel Osoba, wanda a karon farko suka ziyarci kasar.

Bayan isanta kasar tare da mahaifinta, ta bayyanar da cewar wannan ai itace kasa da yakamata ace kowa yana shaukin zuwa, domin kuwa mutanen kasar na da son baki. Kuma kasar nada yanayi mai dadi, ga abinci kala daban daban wanda baka bukatar abinci da aka sarrafa da wasu sinadarai.

A wata tattauanawa da akayi da ita a gidan radiyon Beat99.9fm, ta bayyanar da cewar da tanada hali gaskiya, da zatafison ta zama ‘yar Najeriya, domin taga mutane kasar musamman matasa, nada basira kuma da girmama nagaba. Tana ganin abubuwa kadan matasa ke bukata su zama manyan mawaka a fadin duniya, don suna da basira fiye da yadda ake tunani.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG