Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Cinnma Burin Rayuwar Yau Da Kullun!


Akwai matukar hikima ga matasa idan zasu dinga ware mintoci talatin a kowace rana, don karanta wani labari ko tarihi don kara fahimtar rayuwa. Hakan zai taimaka ma mutun matuka wajen kara fahimtar rayuwar yau da kullun. Haka idan mutane zasu dinga ware wasu lokutta don tunani da duba wasu abubuwa na baya, da wanda suke bukatar gabatarwa da niyar fitowa da hanya da tafi dacewa, da matakin su shima wata hanyace ta fahimtar rayuwa.

Haka yana da kyau matasa su dinga kokartawa wajen yin magana a bayyanar jama’a, wanda hakan na kara goge su, da sanin yadda ya kamata su fuskanci rayuwar yau da ta kullun, da kyautata mu’amala da mutane a kowane hali.

Tattaunawa don fitowa da hanya da tafi dacewa, wani abune mai matukar muhimanci, a duk lokacin da aka samu rashin jituwa, yana da kyau mutane su zauna don maslaha, da fahimtar juna.

Sani da iya magance matsalolin kusa da na nesa, cikin tsanaki na taimakawa matuka wajen iya zaman takewa ta yau da kullun. Samun abokai nagari shima wata hanyace da matasa zasu iya amfani da ita don kara fahimtar rayuwa, da yadda za suyi mu’amala da mutane kowane iri, musamman idan suka tsinci kansu a wasu bangarori na fadin duniya.

Neman taimako ba gazawa bane, illa hakan na kara bama mutun karfin gwiwa a rayuwa, ba wai hakan na nuna gazawar mutun bane, kamar yadda wasu ke gani. Sama rayuwa buri da tsara yadda za’a cinma burin, shima wani abu ne mai matukar muhimanci a wajen sanin rayuwar yau da kullun. Haka tsimi da tanaji wata hanyace don kara nazari a rayuwar yau da kullun.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG