Kokarin bin doka a kasashen da suka cigaba, ba wai abun mamaki bane musamman daga kan kananan yara. Yara tun suna ‘yan shekaru uku 3, ake fara koya musu sanin bin doka da oda. Wani yaro dan shekaru shida 6, da haihuwa ya saka mahaifin shi a cikin wani tarko, mai wahalar fita.
A dai-dai lokacin da yaron suke tafiya da mahaifin shi a cikin mota, don zuwa wajen wankin mota, mahaifin yaron ya karya dokar hanya, inda ya wuce fitilar da ke bada hannu, bayan ta tsaida su. Bada jimawa ba, sai yaron ya dauki wayar uban ya kira lambar 911.
Yana kiran lambar sai aka amsa, yace yana karar baban shi ne, domin kuwa sunzo wajen fitilar hanya, an kuma tsayar da su amma baban shi bai tsaya ba, wanda hakan ya sabama dokar tuki. Yaro dai ya kara da cewar muna tafiya dani da baba na, a cikin motar mamana mai kalan baki, sai babana yaki tsayawa, bayan wutar kan titi tasa ja.
A cewar hukumar ‘yan sanda ta babban birnin Massachusetts, baban yaron ya aikata laifi matuka. Kuma abun da yaron yayi shine dai-dai, ya kamata ace kowa na bin doka da oda. Don haka ana kara jan kunnen iyaye da su bama ‘yayan su tarbiya tagari da yin abun da yaran za suyi koyi da shi na gari.