Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yan Sanda Ta Damke Wasu Tsagera


Rundunar ‘yan Sandan jihar Ogun, ta cafke wasu mutane masu lalata bututun mai a jihar Ogun, a wani samame da suka kai a wurare daban daban a jihar.

Wasu ‘yan tsagera hudu da suke cin Karen su babu babbaka a Ikorodu-Arepo, suma suna cikin wadanda suka shiga hannun jami'an 'yan Sanda.

Wadanda aka cafken sun hada da Pere Ugbozuwa, dan shekara 40, wanda kuma shine sakataren ‘yan tsageran, Audu Tony, dan shekara 39, Ifeanyi Eze, 29, da Ojogo Eziekel dan shakaru 23.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Muyiwa Adejobi, yace wadanda ake zargin suna hedkwatan rundunar ‘yan Sandan na masamman masu yaki da ‘yan fashi domin amsa tambayoyi.

Wannan nasarar da aka samu ya biyo bayan alkawarin da Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Abdulmajid Ali, yayi na sa kafar wando daya da mugayen mutane a jihar Ogun baki daya.

XS
SM
MD
LG