Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Novak Djokovic" Ya Kafa Tarihi A Fagen Tennis A Duniya!


Shahararren dan wasan kwallon “Tennis” Novak Djokovic, ya samu damar lashe kofin zinare, ya zamo mutun na farko da ya lashe kofin gasar sau hudu har na tsawon rabin karni, ciken shekaru fiye da hamsin ba’a taba samun wanda ya cinye gasar har sau hudu ba a jere a jere ba.

An karrama shi da wannan kofin na zinariya, wanda yake ta burin samu. Ya samu wannan nasarar ne a gasar cin kofin a kasar France. Ya bayyanar da wannan rana a gare shi, a matsayin muhimmiyar rana a tarihin rayuwar shi. Yana ganin cewar ya kafa tarihi a rayuwar shi, wanda a cikin iya tsawon wadannan shekarun, babu wanda yayi abun da yayi.

Ya bayyanar da cewar tun a shekarar 1969, da dan wasa Rod Laver, ya taba rike wannan kambun, sai kuma a wannan lokaci gashi ya kawo gare shi. Dan wasan dai ya nada shekaru ashirin da tara 29, da haihuwa a duniya. Ya samu damar lashe wasan Australian Open sau uku, sai na U.S Open shima sau biyu, kana ya rike kambu wanda Federer, Rafael, da Pete, duk basu taba rikewa ba a tarihin wasan su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG