Talakawan kasar Amurka, sun koka dangane da yadda ake kashe makudan kudade al’uma da suke ganin ya kamata ayi amfani dasu ta wata hanyar da suka dace. Wannan kiran ya fito ne a lokacin da aka bayyanar da irin makudan kudade da ake kashe ma jirgin shugaban kasar Amurka.
Shi dai wannan jirgin da ake kira “Airforce One” shine jirgin da zababben shugaban kasar Amurka, ke hawa don tafiye-tafiye a fadin duniya. Wannan jirgin yana da tsare-tsare kamar yadda ofishin shugaban kasa yake a babban birnin tarayyar kasar. Cikin jirgin yana dauke da dakukuna, da ofishin shugaban kasa. Duk a cikin jirgin akwai dakin taro, da akwai yanar gizo da shuagan kasa zai iya ganawa da kowa a fadin duniya. Cikin jirgin yana dauke da wasu motocin da shugaban kasa ke hawa a duk kasar da yaje da ake kira “The Beast” guda biyu wadda basu jin harbi balle bom, sai jirgi mai saukar angulu.
An kiyasta cewar ana kashe ma wannan jirgin kimanin dallar Amurka, dubu dari biyu da shida, da dari uku da hamsin $206,350 dai-dai da naira milliyan arba’in da daya da dubu dari biyu da saba'in 41,270,000. A duk awa daya da yayi yana kunne. Yanzu haka dai an sake bada sabuwar kwangilar kera wani sabon jirgin, don ana ganin wannan ya tsufa. Wannan jirgin na daya daga cikin jiragen da aka fi kashe ma kudi a fadin duniya.