Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Kabarin "Aristotle" Bayan Shekaru 2,400 Da Suka Wuce!


Aristotle nd Alexander
Aristotle nd Alexander

Masana kuma masu binciken abubuwan tarihi na karkashin kasa “Archaeologists” a turance, sun bayyanar da tabbaci da suke da shi, na gano kabarin shahararren masanin “Falsafa” na kimiyyar hasashe a fadin tarihin duniya “Aristotle”

A cewar Kostas Sismanidis, tabbas wannan akwatin da suka gano a karkashin kasa wanda ya kwashe, kimani shekaru dubu biyu da dari hudu 2,400 a cikin karkashin kasa, shine kabarin Aristotle. Shi dai wannan masanin ya taka muhimiyar rawa wajen tarihi a duniya, musamman a fannin binciken kimiyyar nazarin ma’amala da zaman takewa.

Yanzu haka dai masanan suna kara zurfafa bincike a yankin na Macedonia, a kasar ta Greece, inda suke kokarin fadada bincike tun daga shekara ta dari uku da tamanin da hudu 384, kamin zuwan annabi Isah. A iya binciken nasu da suka gano kabarin a kusa da wani tubali mai tsawon tarihi a kasar. Akwatin nada wani kira da basu taba ganin irin shi ba a wannan zamanin. Wannan na daya daga cikin dalilan su na bayyanar da shi a matsayin kabari na mutun da yayi abun da duniya bazata taba mantawa da shi ba, shiyasa kabarin shi ya fita daban.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG