Sophie Tanner, wata budurwace mai shekaru talatin da bakwai 37, da haihuwa. Ta kasance mace da bata da wata damuwa a rayuwar ta, sai dai duk cikin tsawon shekarun ta bata da saurayi. Ta tambayi kanta cewar wai kodai bata da kyaune? Babban burinta shine taga yau tayi aure da wanda take so. Bayan kwashe sama da shekaru ashirin 20, tana jiran miji, amma bata samu ba.
A dalilin rashin saurayi, ta yanke shawarar ta auri kanta da kanta. Duk da dai aure alkawali ne tsakanin mace da na miji, to ita batada na miji, amma tana ganin zata iya yima kanta alkawali da kanta. Ta siyo zobe na kimanin naira dubu ashirin, kana ta gayyaci ‘yan uwanta da abokan arziki suzo auren ta.
A wasu al’adun aure, uba kan rike amarya ya ratsa ta wata kofa, kamin ya mikata ga malamin da zai daura aure, tsakanin ta da mijin ta, itama wannan amaryar Tanner, ubanta Mr. Malcolm mai shekaru 68, ya riketa inda ya gabatar da ita ga mai daura mata aure da kanta.
A tabakin ta “Auren kaina ba wai abu da naso yi bane, kawai saboda ban samu maiso na bane, yasa na yanke wannan shawarar” ta kuma kara da cewar “Auren kaina da nayi wani abune da zai ciremun tunanin cewar bani da aure, yanzu zan dinga ganin kaina kamar sauran ma’aurata.”
A cewar jaridar Mirror ta kasar Ingila, yanzu haka dai Tanner, tana bukin cika shekara daya, da auren kanta da tayi. Kuma tana kokarin jawo hankalin wasu mata, da suma su dauki wannan a matsayin hanyar magance matsalar rashin masoya.