Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Shaye-Shaye Kawai Ke Assasa Ciwon Tabuwar Hankali Ba!


Russian President Vladimir Putin aims a sniper rifle during a visit to the Patriot military exhibition center outside Moscow, Russia.
Russian President Vladimir Putin aims a sniper rifle during a visit to the Patriot military exhibition center outside Moscow, Russia.

Wasu kadan daga cikin alamu da ke nuna alamun kamuwa da ciwon hauka. Wani masani kuma mai zurfafa bincike a kan dabi’un dan’adam. Dr. Adeoye Oyewole, ya bayyanar da wasu alamu da suke bayyanar da cewar mutun na kusantar tabin hankali. Ya bayyanar da cewar ba kawai shaye-shaye ke assasa tabin hankali ba.

Tabin hankali na daya daga cikin cuttutuka da akafi kyamar mai dauke da ita a ko ina a fadin duniya. Musamman a kasashen Afrika, inda ba’a cika taimakama masu dauke da wadannan cuttutukan ba a cikin gaggawa. Musamman idan basu da ‘yan uwa da suke da karfi, domin kuwa gwamnatoci basu cika bada karfi a wajen taimaka ma masu irin wannan halin ba.

Sau da dama idan mutun ya taba kamuwa da irin wannan cutar, koda ya warke za’a ga cewar ba’a basu aure ko daukar su aiki, ana kyamar su. A duk lokacin da ka ga mutun yana yawan kebe kanshi daga cikin jama’a, kuma baya son magana, da dai kokarin yi ma kanshi abu batare da neman taimakon wasu ba, a lokacin da ya kamata ya nema don gazawar dan'adam. Ko kuma aga mutun bai damu da tsaftar jikin shi, ko wajen da yake zama ba, to lallai akwai bukatar duba irin wadannan mutane. Haka kuma a duk lokacin da akaga mutun yana shan magunguna da ba likita ya rubuta mishi ba, to a kokarta nesanta shi da irin wadannan shaye-shayen, don gujema kamuwa da tabin hankali.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG