Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nakasa Bata Hana Mutun Zama Wani Abu Rayuwa!


Wani yaro dan shekaru 16 a nan kasar Amurika, da aka haifa da wata irin matsala wadda take dakile basirar yara, yayi wata rawar gani. Shi dai wannan yaron me suna Malika, ya kasance bai fara magana ba har sai da ya kai kimanin shekaru 5, wanda kuma baya fahimtar kome aka koya mashi, amma daga bisani, bayan ya kai wani matakin rayuwa, ya kirkiri wata hanya da take taimakama yara da malamai wajen fahimtar karatu a saukake.

Wannan tsarin na shi da ya kira “Gwarzon Duniya” wato abun da yake nufi shine kowane yaro na iya zama wani abu musamman idan ya lura da yadda rayuwa ke gudana. Sai yace, kowane yaro ya tashi da zummar cewar zai yi abu don taimakama wani badan kanshi ba, tahaka zai iya zama gwaro da kowa zaiyi kokarin koyi da.

Babban abun la’akari da shi a nan shine, ya kamata iyaye da malamai su maida hankali wajen koyar da yara wasu darussa da zasu kara samu su kaimi wajen neman zama wani abu. Misalli kamar koyar da Tarihi, Labarai kamar su tatsuniya, al’adun wasu kabilu da kasa, da dai sauran maka mantan su, ta haka za’a iya samun dai-daito wajen zaburar da yara su zama wani abu a rayuwar wasu yaran.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG