Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Biyan Bukatun Iyalansa


A jihar Abia wani ma’aikacin Gwamnatin, ma’aikatar kasa da safiyo, Mr. Nwankwo, ya kasha kansa saboda kasawar sa wajen biyan bukatun iyalansa.

Jaridar Leadership, ta ruwaito cewa an kwashe watani ba’a biya Nwankwo, albashen sa ba, wanda hakan yasa shi tsaka mai wuya wajen ciyar da iyalansa.

Nwankwo, dan garin Ndume a karamar hukumar Umuahia ta arewa, yana da ‘ya’ya hudu biyu a makarantar firamare biyu kuma a makarantar sakadare.

Wata majiya ta fadawa jaridar Leadership, cewa sau tari Nwankwo, kan nemi taimako daga ‘yan uwa da abokan arziki na kayan abinci ko kuma kudi domin ciyar da iyalisa.

A wata takarda da mammacin ya ruta gabanin daukar rayuwarsa da take hannun ‘yan Sanda, yace “ Bani da inda zanje in samo bani da abincin da zan baiwa yara na kuma babu albashi na tsawon watani hudu ayi hakuri tilas ne in aikata wannan.”

XS
SM
MD
LG