Shugaban kasar Australia, Mr. Malcolm Turnbull, shine shugaban kasa na biyar a cikin jerin shugabannin masu daukar mafi yawan albashi a duniya. Yana daukar kimanin dallar Amurka $396,000. Shi kuwa shugaban kasar Austria, Mr. Werner Faymann, wanda yazo a mataki na shida, yana daukar dallar Amurka $343,000.
A cikin jerin kuwa sai shugaban kasar Luxembourg, Mr. Xavier Bettel, ya zama na bakwai, inda kuma yake daukar dallar Amurka, $255.00. Kana firaministan kasar Canada, Justin Trudeau, yana samun kimanin dallar Amurka $253,000 a matsayin albashin shi a shekara.
Shugaban kasar Germany, Angela Merkel, itace ta zama ta tara, inda take daukar dallar Amurka $244,000 a matsayin albashi a shekara. Na goma kuwa shine shugaban kasar Belgium, Mr. Charles Michel, wanda yake daukar kimanin dallar Amurka $239,000 duk dai a matsayin albashi a shekara.