Daya daga cikin mawakan da aka bayyana a zaman mafiya basirara kirkirar waka a wannan zamanin, Prince, wanda yayi suna a fadin duniya da wakoki kamar “Little Red Corvette," ''Let's Go Crazy" da "When Doves Cry," yam utu yau alhamis.
Jami’ar hulda da jama’a ta Prince, Yvette Noel-Schure, ta shaidawa kamfanin dillancin labaran AP cewa yau aka tsinci gawarsa a cikin gidansa dake bayan garin birnin Minneapolis a nan Amurka.
Babu wani karin bayani da aka samu na yadda Prince ya rasu.
Prince, dan asalin Minneapolis, ya yi suna a duniya a cikin shekarun 1970 zuwa farko-farkon 1980 da wakoki kamar “Why You Wanna Treat Me So Bad?" da "I Wanna Be Your Lover," sannan yazo yayi farin jinni matuka da wasu faya-faye kamar "1999" da "Purple Rain."
A shekarar 2004, an shigar da sunan Prince a dakin tarihi na mawakan da suka fi kwarewa a duk duniya a fannin wakokin Rock & Roll.