Suka ce alummar arewa maso gabashin Najeriya suna da nasihohin da yakamata suyi koyi dasu na nuna wa juna kauna da kuma gafartawa ganin irin rikicin boko haram da ya addabi yankin wanda yayi sanadiyyar rayuka da dama da y araba wasu mata da mazajen su ya kuma mayar da dubbanm yara marayu kamar yadda Reverend Father Ngare.
‘’A cikin bisharar Luka shi Ubangiji Yesu Almasihu yace ruhun ALLAH na tare dashi ya zabe shi ya aike shi domin ya kawo shelar bishara ga matalauta, to ashe yakamata kirista su kawo wannan shelar bishara ga matalauta domin sune mafi yawa a cikin duniya musammam a arewa maso gabashin Najeriya, dake fama da fadace-fadace da tashin hankali akwai mutane da yawa wadanda an kokkone gidajen su akwai mutane da yawa da ‘yan uwansu suka rayukan su akwai yara da yawa wadnda sun zama marayu’’
Ga Sanusi Adamu da ci gaban rahoton 1’50