Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Wasan Super Eagles Sun Isa Sansani Don Shirin Wasan AFCON 2017


'Yan Wasan Super Eagles
'Yan Wasan Super Eagles

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafar Najeriya “Super Eagles” Mike Obi, da dan wasan klob din Arsenal, Alex Iwobi, da dai sauran ‘yan wasan kungiyar sun isa sansanin ‘yan wasa. Inda zasu fara atisaye don haduwa da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar kasar Egypt.

Wannan atisayen shirye-shirye ne na fuskantar wasan zakaru na neman shiga gasar cin kofin kasashen Afrika, na shekarar 2017. A cewar mai magana da yawun klob din Mr. Toyin Ibitoye, ya bayyanar da dawowan ‘yan wasan a matsayin wata damace da zata bama ‘yan wasan wuri don su shirya wajen fukantar kasashen Afrika.

Ana dai sa ran ‘yan wasan kwallon kafar Najeriyar zasu hadu da abokan gwabzawan su a filin Ranchas Bees dake garin Kaduna, a ranar 25 ga watan Maris, haka kuma suma ‘yan wasan na Najeriya zasu sake haduwa da ‘yan wasan na kasar Egypt a filin wasa na Alexandria a kasar Egypt din a ranar 29 duk a watan Maris.

Wannan haduwar akwai ‘yan wasa dake bugama wasu manyan klob na duniya wasa, wanda suka hada da Aminu Umar, da Shehu Abdullahi, haka kuma akwai wadanda suke buga wasa a gida kamar su mai tsaron gida Ikechukwu Ezenwa, da Oghenekaro Etebo.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG