Inda rai da lafiya mutun zai sha kallo! Abubuwan ban mamaki da ban al’ajabi basu karema mutun idan yana raye. A kasar Yemen, wata kotu ta yanke ma wani yaro mai shekaru 15, hukunci da sai ya auri Rakuma. Hakan kuwa ya biyo bayan shaidu da aka samu kan cewar yaron ya kwashe tsawon lokaci yana saduwa da rakumar.
Yaron dai ya amsa cewar gaskiya ya kanyi lalata da rakumar, yanzu haka dai rakumar ta haihu, kuma an danganta yaron a matsayin uba ga jaririn da rakumar ta haifa. A cewar wasu manyan mutane, wannan halin da yaron yayi ba dabi’ace da ta dace ba, don haka kada a sake jin irin wannan halin. Kotun dai tayi wannan hukuncin ne don ta tsawata ma yaron da ma masu irin halin. Yaron dai ya nuna nadama da kuma alkawalin hakan ba zai sake faruwa ba , ya roki gafarar kotun.
An dai zartar da hukuncin ne a bayyanar jama’a, hakan dai yasa yaron da ‘yan uwan shi cikin kunya, ya kuma dauki alkawalin wani abu makamancin haka ba zai sake faruwa ba. A tabakin wani malami, yace ya kamata mutane su kokarta wajen tarbiyantar da ‘yayan su. Domin kuwa wannan zamanin da ake ciki, matasa kanyi wasu dabi’u da basu dace da koyarwar addinai ba.