Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimani Sama Da Shekaru "700" Rabon Da Ashiga Wasu Dakuna A Masar


A cikin jerin sarakunan da akayi a masarautar kasar Masar, Sarki Tutankhamun, ya mutu a shekarar 1324 kamin zuwan annabi Isah, bayan ya kwashe shekaru 9 yana mulki, haka kuma ya mutu yana dan shekaru 19, da haihuwa a duniya.

Yanzu haka dai wasu masu binciken kayan tarihi a kasar ta Masar, sun gano wasu dakunan hutawa na sarkin a wancan lokacin. Masu binciken sun samu damar bude bayan mutun mutumin tsohuwar sarauniya Nefertiti, mahaifiya ga sarki Tutankhamun. A cewar ministan binciken kayan al’addu na kasar Mamduh Damati, ya bayyanar da hakan.

Ya kara da cewar suna da yakini kashi 90% da ya nuna musu cewar akwai dakuna guda 2, wanda suna tunani akwai wasu kaya a cikin su, amma tunda wannan mutunmutumin sun kwashe shekaru masu yawa, to yanzu dai za suyi kokari wajen ganin an bude bayan mutunmutumin, don ganin irin kayan da suke cikin dakunan biyu, da kuma komarin duba su da irin amfanin da za suyi a wannan zamanin. Suna kokarin ganin sun bayyanar da abubuwan tarihi, don bama al'uma damar sanin irin rayuwar mutanen da.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG