Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Halin Wasu "Yan-Matan Kesa Su Rasa Samarin Kirki!


A kowane irin lokaci da mace ta kasa samun miji, to lallai akwai abun dubawa a cikin halayyan ta. A matsayinki na mace kin taba kokarin samun namijin kirki amma baki samu ba? Kokarta bin wasu daga cikin shawar’warin nan da suka fito daga masana halayyan dan'adam. Idan har duk yadda kikayi wajen neman miji wanda yake sonki kuma ya damu da ke amma hakar bata cimma ruwa ba, to gwada wadannan abubuwan ki sha mamaki.

Ke mace ce mai tsiwa, fada da kowa, rashin kamun kai, magana da kowane irin mutun, shiga harkar da bata shafe kiba, gulmar kawa ko aboki, yawaita bakinciki don kawarki nada saurayi, ke baki da shi? To fara duba kanki ki gani wai me kikeyi wanda ya sabama yadda sauran mutane ke gudanar da rayuwar su ta halin yau da kullun. Yima kanki adalci wajen bayyanar ma kanki da gaskiya koda kuwa baza kiji dadin yin hakan ba.

Ke maccen cikin gida ce? Baki zuwa makaranta, baki da kawaye da suke zuwa makaranta, kuma duk samarin unguwar ku sun sanki, fara neman saurayi dan wata anguwa ko wani gari, hakan kuma na iya kasancewa ne idan kika ziyarci kawaye da suke wasu anguwa, kuma suke mu’amala da mutane kirki. Daga nan sai kiji amfara tambayar wai ina kawarki ta anguwa kaza? Haka kuma kin iya girki kuwa? Kokarta wajen karanta littatafai da ake koyar da girke-girken zamani, don koya ma kawayenki da suke da samarin da mazajen kirki, daga nan abokan miji zasu fara sanar da abokan su cewar kawar matata ta koya ma matata yadda ake yin abinci kaza, kinga daga nan hanya ta budu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG