Cikin jerin kasashen da sukafi daukan matakan tsaro wajen samar da izinin shiga kasar su, sun hada da kasar India, suna da matsananciyar hanya wajen neman izinin shiga kasar, kamin suma a samu izinin shiga kasar duk a cikin fom da mutun zai cika suna bukatar mutun ya bayyanar da inda yake aiki da kuma sheda.
Kasa ta bakwai itace Thailand, idan mutun dan kasar Ingila, Canada, Amurka, ko Austrailia, ne yana iya zuwa wannan kasar yayi kwanaki 30 batare da ya nemi izini ba. Amma idan mutun zai wuce wadannan kwanakin to sai ya nemi izini kamar kowa a fadin duniya.
Kasa ta takwas kuwa kasar Chad, wanda har ya zuwa yau basu fara bada izini su ta yanar gizo ba, sai dai mutun ya aika da takarda, kuma idan mutun bayajin yaren French, to sai dai ya nemi wanda yakeji kuma mutun sai ya dinga kiran su akai akai.
Kasa Nigeria kuwa itace kasa ta tara wanda idan mutun na neman izinin shiga kasar sai yabi wasu hanyoyi wanda zai nema ta hanyar wasu kamfanoni batare da yabi ta hannun gwamnati ba, kuma mutun zai biya kudi har kashi uku, zai biya kudi ga gwamnatin kasar, kana ya biya offishin jakadanci wani kudi kamin kuma ya biya kamfanin da kema gwamnatin aiki don deman izinin.
Ta goma kuwa itace kasar Sudan, suna da tsari irin na sauran kasashen duniya, amma wani abun mamaki shine kamin kasamu izinin shiga kasar yana iya daukar watanni kamin su amsa maka.