Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiyon Lafiya ta Duniya Zata Bukaci Dala Miliyan 56 Don Yakar Cutar Zika


APTOPIX Guatemala Zika Virus
APTOPIX Guatemala Zika Virus

Wannan cutar dai ta zama abar damuwa ainun musamman a kasashen nahiyar Kudancin Amurka

Hukumar Kiyon Lafiya ta Duniya tace zata bukaci akalla Dala Miliyan 56 don aiwatarda matakan da take son dauka don yakar cutar sauron nan ta Zika da ake ta’allakawa da sa ana haihuwar jarirai da nakkasa a jikinsu.

A yau Laraba ne WHO ta bayyana cewa matakan nata zasu hada da hada hancin masana da abokan aiki da kwararru dsa kayan aiki don agazawa kasashen da wannan cutar ta shiga cikinsu, ta yadda su kuma zasu iya kara maida hankali kan cutar da sauran lahanonin da take janyowa.

Hukumar ta WHO tace izuwa yanzu ta shjiga cikin asusun kudadenta na gaggawa don zaro ‘yan kudaden da zata fara andfani da su wajen tinkarar wannan al’amarin har zuwa lokacinda aka samu kudaden da za’a rarraba wa kasashe da kunguyoyin da zata yi aiki da su wajen wannan fafatika akan cutar ta Zika, wacce ake samunta daga sauro.

Wannan cutar dai ta zama abar damuwa ainun musamman a kasashen nahiyar Kudancin Amurka na Latin, ciki harda Brazil inda ake kiyasin ta kama mutane akalla 4,300.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG