Da badan irin munmunan matakin da na dauka ba, da yanzu dana ya mutu! Mr. George, mai shekaru 59, kuma mahaifi ga Pickering dan shekaru 27, duk mazauna jihar Texas ta kasar Amurka. Dan nashi Pickering, ya kamu da wata matsananciyar rashin lafiya. Wanda sanadiyar hakan yasa ya suma har na tsawon kwanaki, har ta kai ga sai da aka sa mishi wani mashin da yake kula da shi.
Daukar kwanaki da yawa yasa likitocin asibitin yanke shawarar cewar, wannan yaron bazai rayu ba, don haka akwai bukatar a dena wahalar da kai da kudi, kuma sun gaya ma uban yaron da cewar, zasu cire yaron daga kulawar wannan mashin din. Uban yaron George, ya bayyanar da cewar, bai yadda da abun da suke tsammani shine cutar da ke damun yaron nashi ba.
Don haka maganar cire shi daga taimakon da yake samu a wajen wannan mashin din, bai gamsu da hakan ba. Bayan asibitin sun yanke shawarar yin hakan, sai uban yaron yaga cewar abun na gaba da kawai ya rage mishi shine, ya dau mataki da ya dace. Ya shiga asibitin dauke da bindiga ya rike daya daga cikin likitocin da cewar idan suka cire yaron shi, to lallai zai kashe likitan, hakan dai yasa ankwashe kimanin sama da awowi 3, ana takaddama da shi kan cewar yayi hakuri.
Ana cikin hakan sai ga yaron ya fara motsi, hakan dai yasa uban ya bada bindigar, kuma ya yarda an kama shi. Bayan samu lafiyar yaron ya bayyanar da cewar, lallai uban shi ya karya doka, amma dokar da ya karya itace ta jawo mishi ya rayu. Don haka wannan shine ake cema kauna ta mahaifi da da.