Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Dalilai Da Kesa Aure Yin Karko Musamman Ga Sabon Aure


Sirrin ma’aurata da zai sa aure ya wuce yadda ake tunani, wasu masana sun bayyanar da wasu abubuwa da ke da matukar muhimnaci ga sababbin ma’aurata. Idan kuwa har ma’aurata zasu dauki wadannan abubuwan da kuma aiwatar da su, to ba shakka auren su zai zama mutu karaba.

Yana da matukar muhimanci ga amarya da ango da su kayi aure bada dadewa ba, su ware wasu watannin don angwanci, "Honeymoon" a turance, a waje daya, da bayyanar ma juna wasu abubuwa da ya kamata kowa ya kiyaye. Haka ma akwai bukatar ango da amarya su nisanta kan su na ‘yan wasu kwanaki, ko dai ango yayi tafiya ko amarya tayi tafi, wanda hakan zai sa ayi mar-marin juna. Idan rai ya bace a nisanci juna.

Akwai bukatar ma’aurata su fahimci cewar aure kamar sabon aiki ne, don haka kowa a tsakani ya rike aikin shi kwarai da muhimanci, kada yasamu matsala da shugaban shi a wajen aiki daga samun sabon aikin. Haka kuma babu wani tsafi ko suddabaru da zai sa ace ansan halin juma dari bisa dari, don haka sai andinga taka tsan-tsan wajen kyautata ma juna. Babu dalilin da zai sa baza’a zama abokan juna ba, kada wani abu na boyo ya shiga tsakani, akwai bukatar bayyanar da komai ga juna, batare da wasu ‘yan bayan fage na bada shawarar yadda zaku magance matsalar ku ba. Hakan na sa aure ya wuce yadda ba’a taba tsanmani ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG