Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jerin Sunayen Shugabanni Amurka Masu Kudi Kashi Na 3


President Barack Obama at the CEO Summit of the Americas in Cartagena, Colombia, Saturday April 14, 2012. (AP Photo/Carolyn Kaster)
President Barack Obama at the CEO Summit of the Americas in Cartagena, Colombia, Saturday April 14, 2012. (AP Photo/Carolyn Kaster)

A cikin jerin tsofaffin shugabannin kasar Amurka da muke kawo muku da irin abun da suka mallaka. Na goma shine tsohon sugaban kasa Bill Clinton, mafi akasarin kudin shi, ya same su ne lokacin da yake aikin lauya mai zaman kanshi. Haka kuma bayan barin shi mulki ya rubuta littafi mai take “Rayuwa ta” wanda aka siyar da sama da kwafi milliyan biyu. Hakan kuma yakan samu kudi a duk lokacin da aka gayyace shi, yayi magana a wajen taro. Yana da addadin kimanin milliyan $55M, dai-da da naira billiyan dubu dari biyu.

Sai shugaba John Tyler, ya zamo shugaban kasar Amurka, kwanaki 23 da shiga offishin shugaban kasa William Henry, bayan ya mutu, ya samu kudin shine a sana’ar noman taba, kuma yayi aure daga gidan masu kudi. Ya zama na 11 cikin jerin masu kudi, da yake da $51 dai-dai da naira 11,220,000,000.

Sai na 12, shine James Monroe, shima dai tsohon lauya ne mai zaman kanshi, kuma manomi. Yana da $27M dai-dai da naira 5,940,000,000. Sai na 13 Martin Van Buren, haka nan shima lauya ne mai zaman kanshi, kana yana sana’ar dillanci filaye da gidaje, yana da $26M, dai-dai da naira 5,720,000,000.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG