Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyya Kuwa! Shekaru 5 Ga Yaro Dan-Shekara 8 Adalci Ne?


jusitce
jusitce

Mutane da dama sun tsurama wani alkali idon, don ganin yadda zai zartar da wannan hukuncin. Ana tuhumar wani yaro mai shekaru takwas 8, da haihuwa, shi dai yaron malamar ajin su ta fadi cewar yaron yayi mata raini. Yaron ya kir-kiri jirgin takarda, ina ya jefa mata jirgin da ya sauka a jikin ta.

Malamar dai ta bayyanar da wannan a wani matsayi na wulakanci, tsakanin malami da dalibi, tace yayi mata wannan abun ne a bayyanar sauran abokan aikinta malamai. An gurfanar da yaron agaban kuliya, inda lauya mai kokarin kare malamar ya bukaci alkalin da ya tura yaron gidan yari, har na tsawon shekaru biyar 5, bisa aikata wannan laifin.

Wasu na ganin idan aka yanke ma yaron wannan hukuncin, ba’a yi mishi adalci ba. A yayin da alkalin ya shigo cikin kotun, yaron ya tambayi alkalin da cewar mai alkalin yake yi a nan? kuma ya musanta abun da ake tuhumar shi da. Hakan dai ya faru ne a kasar Kuwai, ta daular kasashen larabawa. Al’umma sun sa idon don ganin yadda wannan hukuncin zai kaya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG