Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwanciya Ta Bangaren Dama Ko Hagu Na Inganta Lafiyar Mutun


Bacci
Bacci

A wani bincike da masana kimmiya suka gudanar, karkashin jagorancin wani Farfesa mai suna Mailen Nedergaard, na jami’ar Stony Brook, dake nan kasar Amurka. Sun iya gano cewar yadda mutane ke kwanciya wajen bacci na taimaka musu wajen magance wasu cututuka a tsawon rayuwar su.

A lokacin gudanar da wannan binciken, anyi amfani da wata na’ura da ake duba lafiyar jikin mutun, wadda aka saka a jikin mutane uku, suka kwanta da su. Na’urar ta nuna lokacin da mutun ke kwanciya ta gefen hannu dama ko na haggu, a dai-dai wannan lokacin kwakwalwar mutun ke wanke duk wata cuta da mutun ya samu a yayinda yake gudanar da ayyukan shin a yau da kullun da rana.

Sun cigaba da cewar lokacin da mutun kuwa ya kwanta a kife ko rub-da ciki, wadansu na’urori da Allah ya hallici dan’adam dasu a cikin jikin shi, basu samun damar yin aiki a cikin jikin mutun. Saboda kwanciya lokacin da cikin mutun yake kallon kasa ko sama, yana hana jiki ya samu walwala. Hakan yakan sa mutun ya kamu da cututuka kamar su rawan jiki, farfadiya, cutar mantuwa da dai makamantan su. Don haka suna kara kira da jama’a su kokarta a lokacin bacci su dinga kwantawa ta bangaren dama ko hagu, domin wannan zai taimaka matuka ma lafiyar jikin su a kowane lokaci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG