Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaba-Kyauta Tukwici: Bayan Samun Kyautar Milliyoyi Ya Bada Shima


Alheri gadon bacci, duk wanda ya kyautata ma wani shima zaiga kyautatawa a rayuwar shi. Mr. James Moss, matashi ne mawaki kuma mai-aski, a garin New York, yana da yaro dan shekara 1, abubuwa sun canza mishi a rayuwa, wanda hakan yasa ya bar garin, ya koma wani gari da ake kira Denver.

Tun bayan isar shi garin yake neman gida da zai zauna da yaron shi, bisa tsari na kasar Amurka, idan mutun na neman hayan gida, sai an duba tarihin mutun, idan mutun bashi da sana’ar da zai biya kudin haya, baza’a bashi gida haya ba. Hakan dai yasa ya koma bakin titi yana kwana da yaron shi, rana daya kawai sai ga wani mutun yazo wajen shi, yace mishi, na tambaye ka labarin rayuwa da kyautatawa a rayuwa mai suke nufi?

Ya bashi amsa, bayan nan mutumin ya bashi kyatar sama da dallar Amurka dubu hamsin da biyar $55,000 dai-dai da naira milliyan goma sha biyu da dubu dari daya 12,100,000. Shi dai Mr. Moss, ganin haka yasa ya tafi wani gidan abinci, ya sayi abinci na makudan kudi ya tafi tsakiyar birnin garin, yana ta rabama mutane abincin. Yace hakan shine kawai hanyar da zai bayyana ma Allah, godiyar shi. Ya kuma kara kiran jama’a da su yi amfani da kudin su koda kadan ne, wajen taimaka ma mabukata a lokacin da suke da bukata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG