“Regera” itace sabuwar mota da ba’a taba yin irin ta a duniya ba, ita dai wannan motar tana da wasu abubuwa da babu mota da akayi mata wadannan abubuwan. Itace mota ta farko da ke gudu daga 0-62 mph a cikin sakon 2.8, abun misali a nan shine tana iya tafiya daga Abuja zuwa Kano cikin awa daya 1.
Bata da shan mai ko kadan, domin tana amfani da mai kuma ana cajinta kamar wayar hannu, kana tana amfani da hasken rana. Kuma kudin ta na iya kaiwa dallar Amurka milliyan biyu da dubu dari biyar $2.5 dai-dai da naira milliyan dari biyar da hamsin 550,000,000. Tana da kofofi kamar fika-fiki.
Kana itace mota ta farko a duniya da komai nata kwamfuta ne, ba’a bude kofar ta da hannu, sai dai kawai a dannan abun budewa ko wayar hannu da aka saita ta ta ita, sai ta bude kuma ta kulle kanta. Kudin da za’a iya kashewa wajen tattalin motar kan kai dalla milliyan dubu dari $100,000 kwatan kwacin naira milliyan ashirin da biyu 22,000,000 a shekara.