Mubashra Uddin, mai shekaru goma sha tara 19, ta hallaka ‘yar da ta Haifa harlahira, Ita dai wannan yarinyar tana karatu a jami’a DeVry, amma asalinsu mutane kasar Pakistan ne. Suna zune a karamar hukumar Cool a nan kasar Amurka. Tun bayan samun cikin ta, ta sanarma saurayin ta da wata kawar ta, cewar wannan abun ya sabama addinin su da al'adun gidan su, amma bata bari iyayenta sun sani ba.
Tana zaune da iyayen ta a gida daya da kanwarta, idan zata tafi makaranta sai ta saka kaya masu tsawo don kada a ga cikin nata, ranar Laraba da misalin 11:45pm na dare, sai ga nakuda ta kama Mubashra. Ta samu ta haifi yarinya, jim kadan bayan haihuwar, sai taji tafiyar mahaifiyar ta tana zuwa dakin ta, sai kawai ta buda windo, daga gidan su mai hawa 8, ta jeho yarinyar, domin kuwa tasan da cewar idan iyayen ta suka ga haka, zata shiga cikin wani hali. Domin kuwa wannan ya sabama addini da al’adun su.
Yarinyar dai ta mutu da misallin karfe 12:25 na dare. Wani mutun ya tsinci yarinyar tana nunfashi, ya kira hukumar ‘yan-sanda. Yanzu haka dai ana tuhumar yarinyar da laifin kisa. A halin da ake ciki yanzu haka tana asibiti kwance, amma bayan ta samu sauki za’a gurfanar da ita gaban alkali don yanke mata hukunci.