Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Cigaba Na Samuwa Ne Kawai Idan An Cire Son Kai


Yunana Ahmed
Yunana Ahmed

A shirin Ilimi mabudin rayuwa na yau, mun samu tattaunawa da Mr. Yunana Ahmed, matashi dan karamar hukumar Das a jihar Bauchi, yana karatun Digirin Digir-gir a fannin da ake kira "Rhetoric,Theory, Culture" a jami'ar jihar Michigan ta nan kasar Amurka.

Wannan karatu da ya keyi, yana da alaka da yadda ake rubutu da zai yi dai-dai da al'adu da dabi'un al'umma. Musamman ga shugabanin a cikin jama'a. Ya fara da bayyana matsalolin matasa a Najeriya, ganin cewar shi ma dan Najeriya, ne kuma malami a jami'a jihar Gombe. Yace mafi akasarin matasa basu da zullumin neman ilimin zamani don dogaro da kai.

Mafi akasarin matasa kan dubi cewar idan nayi karatun nan mai zan zama a rayuwa, sukan manta da amfanin karatun ba wai kawai don cigaban kansu bane, yakamata ace su dinga tunanin yaza suyi su taimakama cigaban kasa bakidaya. Ya jawo hankalin matasa da su gujema duk wasu abubuwa da zasu haddasar da koma baya ga al'umar kasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG