Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

R. Kelly Da Mawaki Dan Najeriya Wizkid Sunyi Sababbin Wakoki


2013 American Music Awards - Show
2013 American Music Awards - Show

Duniyar wakar Najeriya tana kara samun waje a fadin duniya, fitaccen mawaki dan Najeriya da aka fisani da suna “Wizkid” ya samu karbuwa a fagen wakokin kasar Amurka. A karon farko, ya hadu da shahararren mawakin kasar Amurka “Robert Sylvester Kelly” wato “R. Kelly”

Fitaccen mawakin R. Kelly, sun hadu da mawakin Najeriya Wizkid inda sukayi wasu wakoki gomasha hudu 14, wanda ake sa ran za’a fitar da sabbabib wakokin a ranar shadaya 11, ga watan Desambar shekarar nan. Shi dai R. Kelly, shahararren mawakin kasar Amurka ne, da ya bar waka kimanin shekaru da dama, amma yanzu ya sake shiryawa don dawowa fagen waka.

Wannan kan'iya zama wata dama da matasa, masu sha'awar waka zasu maida hankali wajen bayyanar da irin tasu baiwar a duniya. A kasashe da suka cigaba, matasa kan bayyanar da hazakar su wajen daukar kansu, suna aiwatar da abun da suke da sha'awa, sukan yi amfani da wayar hannu wajen daukar bidiyon kansu, sai su saka shi a shafin youtube, daga nan wasu ke gani su gayyace su har su zama wasu abu a duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG