Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekaru 5 Kenan Da Mutane 33 Suka Makale Na Kwanaki 69 A Cikin Kasa


Trapped miners celebrate inside the San Jose mine in Copiapo, Chile
Trapped miners celebrate inside the San Jose mine in Copiapo, Chile

Kimanin shekaru biyar 5, kenan da suka wuce, daukacin mutane a fadin duniya suka shiga cikin halin dar-dar, a dai-dai lokacin da wasu mutane talatin da uku 33, suka makale a cikin wani kogo, lokacin da suke hako arzikin kasa. Wannan abun dai ya faru ne a yankin San Jose a kasar Chile, mutanen dai sun zauna cikin wannan yanayi har na tsawon kwanaki sittin da tara 69, babu wanda ya iya kaiwa inda suke.

Mahaka arzikin kasan, sun gina rami da yakai kimanin zurfin murabba’in tafiya dubu biyu da dari uku 2,300, wannan abu da ya faru ya dauki hankalin baki daya duniya da irin yadda za’abi wajen ciro su.

A dai wannan lokacin kimanin gidajen talabishin na duk duniya sun isa wajen, wanda sukayi aiki bada rahoto na awowi ashirin da hudu 24, babu bacci har na tsawon kwanaki 69, don bayyana ma duniya irin halin da mutane ke ciki. Wanda daga baya ansamu ceto ran wasu daga ciki, wasu kuwa rai yayi halin nashi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG