Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar China Ta Yarda Mutun Ya Haifi 'Yara 2 Kacal A Tsawon Rayuwar Shi


Kasar China, itace kasa da tafi yawan mutane a fadin duniya, yawan mutane a kasar sun kai kimanin billiyan daya da milliyan talatin da bakwai 1.37B, Shekaru da dama da suka wuce , kasar ta China, tasa dokar adadin yaran da kowa zai Haifa a tsawon rayuwar shi a kasar.

Mutun bashi da izinin wuce haihuwar da daya 1, a da, amma yanzu hukumomi a kasar sun sassauta takunkumin, da cewar mutane kan iya haihuwar ‘yaya biyu kacal. A nasu ganin yawan mutane a kasar shi zai iya kawo musu koma baya a tattalin arzikin a kasar.

A tabakin mataimakin shugaban ma’aikatar lafiya da kidayan mutane, Mr. Wang Pei’an, ya bayyanar da cewar, kimanin mata milliyan casa’in 90 ne aka basu damar sake haihuwa, wadanda shekarun su suka kai daga 40 zowa 49. Dalilin yin hakan shine, wasu daga cikin su baza su iya haihuwa ba koda suna so, wasun su kuwa basu iya wuce kara daya, don shekarun su sun ja.

Kamun wannan canjin na dokar, kimanin mutane milliyan hamsin 50, ne da ke zaune a kauyuka, ke da damar sake haihuwa na biyu, suma bisa dalilin sun haifi na farko mace, shiya sa aka basu damar su sake haihuwa ko sun yi dace da samu da na miji.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG