Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kunsan Kasar Da Tafi Cigaba A Tsabar Bincike Kuwa?


Kere-kere na daya daga cikin abubuwa da ke tallafawa kasa wajen cigaba, amma kamin a samu hakan, kasashen nada hakkin samar da duk abubuwa da ake bukata don samun irin cigaban da ya kamata. Samun irin wadannan guraben da damar, sun rataya ne a kan al’uma da kamfanoni masu zaman kansu.

Abun da ake magana akai a nan shine, akwai bukatar samar da cibiyoyin gudanar da bincike na kimiyya da fasaha masu inganci, kana da saka hannun jari don zurfafa bincike da ciyar da shi gaba. Hakama akwai bukatar bama matasa kwarin gwiwa, da basu tsaro don gudanar da bincike da ya kamata ayi amfani da sakamakon binciken wajen ciyar da kasa gaba.

A wani bincike da aka gudanar da ke nuni da cewar wasu kasashe goma sha biyu 12, sune su kafi kowanne kasashe a duniya himma wajen bincike da amfani da fasahar su wajen ciyar da kasar su gaba. Ta farko itace kasar Ingila, sai kasar Taiwan, sai kasar Denmark, sai kasar Singapore, kana da kasar Netherlands, sai kasar Sweden, haka ma da kasar Germany, sai kasar Japan, suma kasar Amurka ba’a barsu a baya ba, kana da kasar Israel, da kasar Finland, ta karshe itace kasar Swetzerland.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG