Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sananniyar Mawakiya "Lady Gaga" Ta Dau Alwashin Barin Waka


67th Primetime Emmy Awards - Show
67th Primetime Emmy Awards - Show

Shaharariyar mawakiyar nan ‘yar kasar Amurka, wadda akafi sani da suna “Lady Gaga” ta sanar da cewar tabar waka har iya tsawon rayuwa ta. Dalilan da ta bada kuwa sun hada da yadda tace, bata jin dadin yadda mutane suka maida rayuwa ba wata abu ba.

Sau da yawa bata jin dadin yadda idan taje wajen taro, zata dinga gaisawa da mutane, da daukan hotuna, ko kuma tazama wata ingin din kera kudi, domin duk lokacin da tayi ma kamfani tallar wani abu da suke sayarwa, za’a dinga bata duki. Bayan ita kuwa bata lokacin kanta. Ta gaji da yadda take shiga jama’a ana daukar hoto, wanda tana ganin cewar yakamata tayi fiye da haka wajen taimaka ma mabukata.

Ta kara da cewar a wasu lokutta bata samun yin abubuwa da take so a rayuwar ta, bisa dalilin mutane basu barin ta yin abun da take so. Amma tana ganin idan ta bar waka, duk lokacin da ta koma gida zata iya duba rayuwar ta taji dadi, da kuma duba cewar wata taimaka ma. Domin yanzu sau da dama mutane kanyi karya, musamman ma da wannan wayar ta zamani. Harkar kimiyya da fasaha za’a iyacewar, an kawo zamani ne kawai na rashin gaskiya ga wasu mutane. Wadanna dama wasu sune dalilai da suka sa ta dau alkawalin barin waka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG