Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-Mata Kyale-Kyalen Duniya Wanda Sai Dasu Ake Zaman Lafiya


Bilkisu Umar Aliyu, da ke karatun digiri na biyu a nan kasar Amurka, ta cigaba da bayyanar da amfanin ilimin ‘yaya mata. Abunda ya karfafama ta gwiwar yin karatu mai yawa shine, mahaifiyar ta a kullun burin ta shine tayi alfahari da ‘yayan ta akan tarbiyar data basu dakuma kokarin da suke yi a wurin karatu su. Sannan tanason tayi karatu ne domin ta kawo canji na ci gaba a jihar ta har da kasa baki daya. Tana so ta wayarma matasa kansu dacewar duk abunda mutun yake nema zai iya samu idan ya dage ya nema. Ba abunda yake zuwa da sauki kuma ba abunda yafi karfin Allah. Kwazo, naci, da bin gurinka zai iya kaika kowane matsayi a rayuwa. Zata so ta ganar da matasa yadda zamu iya kawo ci gaba a al’ummar su.

Shawarar da za taba iyaye akan barin yaran su hardai mata suyi karatu ko subarsu suje har kasar waje wurin karatu shine, iyaye sugane cewar ilimi yanada umfani. Ilimin ‘ya mata ilimin al’umma ne. Idan mace ba tada ilimi ba zata iya taimakon kanta ba, bale yaran ta bale mutanen da take tare dasu. Fitar ‘ya mace kasar waje karatu kuma idan mutun ya yadda da ‘yarshi, ya bata tarbiya ta addinin musulunci, ta fahimci cewa a duk inda take Allah daya ne, toh zata kula da kanta. Abun nufi shine, kar asama yaro jin tsoron mutun ko ganin idon mutun a zuciya, asa mishi jin tsoron Allah don asamu dacewa.

Kiran ta ga mata matasa shine, suyi kokarin neman ilimi a duk inda zai kai su. Su sani dacewa badon sunyi aure ba shikenan rayuwar su ta kare ba, a’a a lokacin ma tafara. A lokacin ne zasu bukaci ilimin zama da miji, da mutane, da taimakon yaran su, idan suna tasowa da kuma al’ummar su. Domin kuwa itama tana da aure, sannan tana digiri na biyu yanzu haka, kuma Insha Allahu ba’anan zata tsayaba. Idan ma mace batada sha’awar yin aiki, ilimin ta zai taimake ta gurin tafiyarda kasuwanci da duk wata hanya da zata iya nemama kudin kanta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG