Klondike, sunan da akayi ma wata dabba “Polar Bear” ne, su dai dabbobin a na samun sune a kasashe masu yanayin sanyi da dusar kankara. Suna da yanayi daban da sauran irin su, musamman ana iya banbanta su da kalan jikin su. Wanda su Polar Bear, jikin su fari ne tas.
Ita dai Klondike, Itace farin bear da tafi kowccen yawan shekaru a kasar Amurka. Ta mutu tana da shekaru talatin da hudu 34, ita dai dabbar tayi fama da rashin lafiya ne, wanda duk maganin da akai mata bata samu sauki ba, a cewar hukumomin gidan Zoo na garin Philedalphia dake kasar Amurka.
Tun bayan kawota wannan gidan zoo din, shekaru talatin 30, da suka wuce, mudai a matsayin mu na ma’aikatan wannan gidan, munji dadin zaman ta da kuma irin yadda take wasa da yara idan su zo gidan. Duk kusan rayuwar ta tayi shi ne cikin daki mai sanyin kankara. Wanda idan kuma lokacin yanayin kankara yazo sai ta fito waje.