Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Satar Bayanan Sirri Abu Ne Mai Sauki Ta Wayar "Smart Phone"


Russia NSA Surveillance
Russia NSA Surveillance

A wani rahoto da hukumomin leken asiri na duniya suka fitar da ke cewar, suna da dubaru da dama da zasu iya kwashe bayanan sirri na mutum, daga aikawa da sakon kar ta kwana (tes), wanda babu abun da mai wayar zai iya yi, a ta bakin Mr. Edward Snowden.

Edward, wani ba’Amurke ne mai ilimin kwamfuta da ajiye bayanan sirri, ya dai bayyana ma manema labarai cewar, masu leken asiri na kasar Burtaniya, suna da wasu kayayyakin aiki da zasu iya sauraren duk wata hira da mutun kanyi a wayar shi da kuma nadar bayanan shi a kowane lokaci suke da bukata.

Abun da kawai suke da bukata shi ne su aika ma mutun da sako, musamman ma ga masu amfani da wayar da ake kira "Smart Phone" wato wayoyin zamani. Daga nan zasu samu damar ganin kyamara, da duk wasu maganganu da mutun yayi, wadannan kayan aiki da ake kira “Smurf Suite” a turance, kowane mutun na da nashi suna. Sukan iya kunna waya da kuma kashe ta a kowane lokaci suka bukaci hakan.

Don haka mutane su san irin maganganun da za su dinga yi, da kiyayewa wajen aikawa da sako, kana akwai bukatar mutane su san da wa suke magana akowane lokaci. Idan kuma mutun na da wani abu da baya so wasu su gani, sai ya san yadda zai dinga ajiye abubuwan shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG