Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ilimin Kimiyya, Fasaha Da Lissafi A Saukake


Jetlag (www.google.com)
Jetlag (www.google.com)

Amfani da komfuta mai sarrafa aiki da jimla abu ne da ya ke da dan rikitarwa, baya ga abun da aka saba na amfani da kimiyyar fasahar sarrafa jimla (Quantum Physics), bamu da tabbacin sanin yadda wannan komfutar tafi wadda aka riga aka saba da ita saurin sarrafa aiki.

Wannan ya zo ne a cikin wani bincike da masana suka gudanar, cikin su har da wani jigo a ilimim kimiyyar Physics, Mattias Troyer, inda yayi ikirarin cewa komfuta mai aiki da adadin jimla ba ta zarta komfuta da aka saba da ita ba kan aiki a muhimman bangarori. Haka kuma masanin kimiyyar Physics, John Martinis, wanda kamfanin Google ya dauka watanni biyu baya don aiki a dakin binciken ta na komfuta mai sarrafa aiki da jimla ta D-Wave, shi ma yana cikin wadanda suka gudanar da binciken, kuma ya musanta hakan, amma tun wannan lokaci ba wani sahihin gwaji da aka gudanar a kan wannan fasaha.

Amma kamfanin Google da wasu da suka sanya hannun jari a aikin, suna zaton fasahar sarrafa aiki da jimla (Quantum Computing) ita ce hanyar samun abu mafi inganci na warware matsaloli. A shafin su da suka buga, inda suka fara sanar da shirin, sun danganta matsalolin da suka jibanci fasaha da kamar kokarin gano can karkashin kasa da ta kunshi kwari da tudu, maimakon gwada tsawon daki daki kamar yadda aka saba, suka ce sarrafa aiki da jimla zai bi ta gefen tsibirin yayi rami yaga wane bangare ne yafi zurfi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG